Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu.
A yanzu dai korafe korafe sun yi yawa dangane da yadda masu Yabon Annabi su ke gudanar da harkokin su, musamman ma dai mata wadanda a kullum su ke kara kwararowa cikin harkar.
Hakan ya sa jaridar dimokuradiiya ta ji tabakin daya daga cikin wadanda suka dade a cikin harkar wato Malam Bashir Dandago, domin jin yadda a matsayin su na iyaye a ciki harkar, amma suka bari wadannan abubuwan su ke faru.
A cikin tattaunawar Jaridar Dimukaradiyya tayi da Bashir Dandago ya fara da cewa, “To ai su matan da suke waka a yanzu kaso 80 cikin 100 ba su su ke rubutawa ba, mazan ne dai su ke rubuta musu, kuma su ne Shehunan su.” Inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun kashe Mutane 36 a Fulatu, tare da jikkata wasu da dama
“Kuma wani lokacin idan an dauke su ma zuwa wani gari da su za su tafi. Shi ya sa Harkar take nema ta lalace, saboda shigowar Mata. Amma dai gaskiya tun farko mun yi fafutuka a kan lallai kada su shigo, saboda mun san akwai Matsaloli, kuma gashi sun shigo har suna neman su kwace abin.” A cewar shi.
” Kuma babbar matsalar da a ke fuskanta ita ce, yawaicin su duk matan aure ne. Mace da auren ta za ta fito ta rinka rera waka, bayan muryar ta al’aura ce. Haka za su saka kananan kaya kuma su fito suna yin waka,”
Kazalika ya ce, “Don haka akwai bukatar gyara a nan, domin ka san babu wani abu da za ka yi shi wanda Shaidan bai shigo cikin sa ba, ballantana harkar da aka ce an shigar da mata a ciki. ” a cewar Bashir.
Daga karshe ya yi kira ga masu yabon Annabi, da su saka tsoron Allah da koyi da Manzon Allah S A W, a cikin Lamuran su na yau da kullun.