• Babban Kotun ta tarayya zata yanke hukuncin kan karar da a kashiga gaban ta kan Atiku Abubakar.
• “Bazan iya cewa komai ba kan batun a yanzu, sabida ba sanar dani ba kan batun sai a jiya laraba” inji Wanda ya shigar da kara.
• Alkan Kotun ya bai ji dadin hakan ba, kuma ya sanya ranar 27 ga watan satun ba domin yanke hukuncin.
Babban Kotun tarayya da ke Abuja ta Sanya ranar Alhamis 27 gawatan Satunba shekarar nan, domin sauraran karar wata kungiyar cimma muradun African, da ta shigar a gaban ta, kan kalubalantar kasance war tsohon shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar dan Nijeriya.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN, ya ruwaito cewa, kungiyar ta shigar da karan ne, tun a shekarar 2019, inda da take kalubalantar tsayawa ta karan Shugabancin kasar nan, da Atiku Abubakar ya yi.
Lokacin da aka fara tuntubar wanda ya jagoran ci shigar da karar Mr Akinola Oladimeji a gaban Kotun a yau Alhamis, ya bayyana wa Kotu ce wa, ba a shirye ya ke ya fara batu a kan lamarin ba.
Olamide ya bayyana wa Kotun cewa, “a jiya laraba ne na san da za a zauna a kotu, kan batun a yau Alhamis, Wanda tunda fari an tsara zaman ne a ranar 20 ga watan Satunba” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gaskiyar lamari kan diban sabbin jami’ai a hukumar kiyaye haddura
Dun haka, nan take Mai shiri’an Kotun Inyang Ekwo ya bukaci a magatakaddan Kotun, da ya binciko kundun karar, domin duba ko an sanar da dukka bangarorin a kan lokaci dangane da zaman.
Daga bisani dai, Mai shari’an Kotun ya ce, baiji dadi ba na rashin kai bayanan zaman ga dukkannin bangarorin a kan lokaci, wanda ya kawo ce-ce-ku-ce.
Inda a karshe Alkalin Kotun ya dage sauraran karar har zuwa ranar 27 ga watan Satunba shekarar nan, Wanda Kuma a cewar shi, shine lokaci na karshe da ya sanyawa wannan karan.