Kasa da watanni biyu akai ga cikar wa’adin mulkin wannan gwamnati ta shugaba Buhari, amma kawo yanzu Dailyreporters24 ta ruwaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza cika manyan alkawuran yakin neman zabensa.
Daga ciki akwai batun fitar da miliyoyin ‘yan Najeriya daga kangin talauci da samar da ayyukan yi miliyan uku a duk shekara.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus
Bayanan da aka samu daga cibiyoyin da abin ya shafa sun nuna cewa an samu karin ‘yan Najeriya da suka rasa ayyukansu.
Yayin da wasu kuma suka kangin fama da talauci a karkashin gwamnatin jam’iyyar APC idan aka kwatanta da yadda al’amura suka kasance a shekarar 2015.
Sai dai wasu masu lura da al’amura na ganin ya kamata gwamnatin shugaba Buhari ta yi aiki mai kyau, amma sun kara da cewa asarar ayyukan yi da karuwar talauci ba Najeriya kadai ba ce.
Sun bayyana cewa wasu manyan abubuwa guda uku da suka dauki gwamnatin Buhari ba-zata sun hada da faduwar farashin man fetur daga shekarar 2014 zuwa 2017, lamarin da ya jawo raguwar kudaden shiga da gwamnati ke samu, lamarin da ya janyo koma bayan tattalin arziki a shekarar 2016.
Daya daga cikin muhimman alkawurran yakin neman zaben shugaban kasar a shekarar 2015 shine magance matsalar rashin aikin yi da talauci a kasar, wani bangare na samar da ayyukan yi miliyan 3 a duk shekara.
A wani labarin kuma: Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba
Gwamnatin jihar Kano ta shirya taron addu’oi ga gwamnonin da aka zaba a kasar nan dama sauran shugabanni da kasa baki daya.
Gwamnan Jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya jagoranci taron addu’ar na makaranta al’qur’ani wanda ya gudana a dakin taro na Afirka House dake gidan gwamnatin Kano a yammacin asabar dinnan, inda yace bisa al’ada sun saba shirya taron yin addu’a a jihar nan don neman dorewar zaman lafiya da karuwarb arziki.