Ousman Dambele dai hana ɗaya daga cikin jerin ‘yan wasan da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta sayo domin su bayar da gudun mawa a gasanni daban-daban da ƙungiyar take fafatawa a kowacce kakar wasa. Itadai Barcelona ta sayo Dambele daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Brussia Dortmund na ƙasar Jamus.
Sai dai bayan zuwansa Barcelona ya gamu da wata matsala ta tafiya rauni akai-akai ganin yadda bayayin cikakken wata guda da lafiya batare daya tafi jinya ba, wani lokacin yakan tafi doguwar jinya inda wani lokacin kuma yakan tafi gajeriyar jinya.
A wasan da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta fafata da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus a gasar zakarun nahiyar turai Dembele ya sami nasarar jefa ƙwallo. Wadda ita ƙwallon daya jefa itace ƙwallon daya jefa ta shida a gasar zakarun nahiyar turai tun bayan zuwansa Barcelona.
A gasar zakarun nahiyar turai dai ya jefa ƙwallaye guda shida, sai dai daga cikin jerin ƙaallayen da Dembele ya jefa, ƙwallaye guda 5 dukkaninsu ya cisu ne da ƙafarsa ta dama, sannan kuma ƙwallo guda 1 ya sami nasarar jefa tane da ƙafarsa ta hagu.
Shin ko wannan kakar wasan ta 2020 zuwa 2021 Dembele zai bugawa Barcelona wasanni batare da yaje jinya ba kamar yadda ya saba a baya?. Lokaci ne dai kawai zan bambance hakan dangane da hakan. Yanzu dai aka fara fafata sabuwar kakar wasan ta 2020 zuwa 2021.