Wani bincike da tashar BBC ta gudanar ya nuna yadda yan siyasa ke wa-kaci-wa-tashi da kuɗaɗen fansho, na ma’aikatan da suka yi ritaya kenan.
Binciken wanda shirin BBC mai Africa Eye ya shafe wata biyar yana gudanarwa, ya biyo bayan shigar burtu ne da mai aike rahotanni kana mai gabatar da shirye-shirye a Jihar Cross Rive Obaji Akpet ya yi ne.
Obaji Akpet ya ce mahaifiyar sa wacce likita ce mai ritaya, ta gaza samun fanshon ta a ka lokaci har sai bayan da aka umarce ta da ta bada na goro ga jami’an dake aiki a ɓangaren kula da harkokin Fansho, gabannin fara karbar tata.
Cikin wani bidiyon sirri da Obaji ya naɗa, ya nuna yadda wata ma’aikaciya ke amsar kudade nasha-nasha, yayin da wasu manyan Manajoji ke tsumayar nasu kason gabanni a duba duk wata takardarta ta Fansho.
Kamar yadda shirin na BBC Africa Eye din ya bankado, ya ce duk da irin wannan gwagwarmaya da Mahaifiyar shi ta yi, amma hakan bai sa ta fara samun Fanshon ta a kan lokaci har sai bayan kimanin wata biyar, al’amarin da ya jefa rayuwar ta cikin matsi da yanayi na rashin kuɗi.
Kazalika binciken na BBC ya gano cewa akwai wasu mutane kimanin dubu guda da aka dakatar da fanshon su, a abinda gwamnati ta kira cewa ba sa raye.
Sanarwar BBC ta ce “Mun gano yadda gwamnoni ke tara wa kan su kudaden fansho wanda ya wuce misali da karin alawus-alawus, a hakan ma bai ishe su ba har suna shirin sake yin ruf-da-ciki da wasu kudaden ta hanyar bijiro da wata doka da za ta sauya tsarin”
“Kamar yadda wani dan siyasa ya shaida mana, abinda kawai gwamna daya ke dauka a matsayin kudin fansho, zai iya biyan albashin malamai sama da dubu hudu.