Youri Tielemans ya jika wa Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea gari bayan da ya jefa kwallo daya tilo da ya kai ga Leicester City lashe kofin FA na ƙasar Ingila a karon farko.
Dan wasan dan kasar Belgium ya jefa kwallon ne da wani kyakkyawan bugun da ta durfafi kusurwan Chelsea yayin da wasan ya dauki zafi cikin minti 63 a filin wasa na Wembley.
Wannan kwallo ya sa Brendan Rodgers murna bakin har kunne tamkar zai shiga filin kece rainin, to amma ga magoya bayan Leicester City kuwa jikin su ya kasa yin daidai har sai bayan da alkalin wasa ya karkare karawar.
Wannan dai shine karon farko kenan da Leicester City ta lashe wannan gasa tun bayan 1969.