Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle ya bayyana cewa akwai kyakkyawar alaka tsakanin sa da gwamnatocin Jihohin Katsina da Sokoto masu makwabtaka da jiharsu, ta fuskar aiki tare wajen tabbatar da tsaro da yaki da yan bindiga.
Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da sashin Hausa na BBC, a birnin Glasgow dake ƙasar Scotland, yayin taron sauyin yanayi da ake kokarin karkace shi a yau.
Ya kara da cewa daga matakin kulle manyan kasuwannin da ya dauka za a fahimci cewa akwai alakar aiki a tsakaninsu, domin kuwa suma sun dauki makamancin wannan mataki.
Matawalle ya ce ‘kaga bayan na rufe wasu daga cikin manyan kasuwanni masu ci mako mako, suma sun dauki irin wannan matakin, sannan ga batun katse layukan sadarwa suma dai har ila yau sun dauki wannan mataki a wasu yankuna na Jihohin su.”
Dangane da tambayar da akai masa cewa shin ko akwai wani yunkuri da yake wajen taimakawa jami’an tsaron jihar?
Ya bayar da amsa cewa yana wannan kokarin matuka, domin kuwa da hawansa gwamna sai da ya samarwa da jami’an tsaron karin motocin sintiri duka dai da nufin basu kwarin gwiwa da kuma kawo karshen matsalar data addabi jihar.