Shirin tallafawa masu karamin karfi wadanda annobar corona ta tagayyara tattalin arzikinsu wato KANO CARES project ya raba kayan noma da kadarori ga masu karamin karfi da marasa galihu 1000 a jihar Kano.
Jami’in kula da ayyukan shirin na Kano Malam Rufa’I Halilu ne ya bayyana haka a lokacin mika kayayyakin ga wadanda suka ci gajiyar tallafin a jihar, inda ya bayyana cewa shirin yana amfani da tsarin ci gaban al’umma (CDD) wanda ke ba da dama ga al’umma domin inganta kasuwancin su.
Malam Rufa’I ya ce rabon kayayyakin ya zo a dai-dai lokaci da ya dace musamman a yanzu da wasu manoma suka fara shuka a yankunansu.
A sanarwar da jami’ar yada labaran shirin a Kano Shafa’atu Sa’id Karaye ta fitar a yau, ta ce Rufa’i ya tabbatar da cewa shirin Kano CARES zai ci gaba da sanya farin ciki a zukatan masu kananan karfi ta hanyar basu tallafin da zasu dogara da shi don bunkasa tattalin arziki su.
Ya kara da cewa shirin na Kano CARES na samun tallafin Bankin Duniya da gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jihar kano kuma an yi shi ne domin taimakon masu karamin karfi da marasa galihu a cikin al’umma musamman wadanda annobar cutar covid19 ta tagayyara.