By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar dake kula da shirin Npower ta fara shirin biyan alawus-alawus na watan Oktobar shekarar 2021.
Wani Jami’in kula da shirin Npower a jihar Kogi, ya bayyana cewa kafin ranar 8 ga watan Junairun da muke ciki na shekarar 2022, duk wadanda suka ci gajiyar shirin Npower Batch C1 za su karbi alawus din su na watan Oktoba.
A cewar majiyar, wacce ta yi magana game da yanayin, ta bayyana cewa an fara biyan kudaden alawus din na Oktoba da Nuwamba a ranar 31 ga watan Disamba, 2021.
“An cire tsarin biyan watan Nuwamba sa’o’i kadan bayan an fara shi.
Kazalika “Cire biyan kuɗi na Nuwamba wanda aka ƙara a baya zuwa shafin biyan kuɗi an yi la’akari da cewa bai dace ba bayan an yi nazari a hankali don hana kuskure tare da tabbatar da hanyar biyan kuɗi kyauta”.
Ya kuma shawarci wadanda har yanzu suke fuskantar matsalar biyan su watan Satumba su tuntubi hukumar NASIMS dan karin bayani.
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro daga wasu da suka ci gajiyar shirin na NPower wadanda har yanzu basu sami alawus din su na watan Satumba ba, wand ake alakanta hakan ga matsalar bankuna da kuma ranar haihuwa na bayan asusun ayarsu.