Gwamnatin jihar Zamfara, ta bayyana cewa shirin killace Fulani da aka fi sani da RUGA da za a yi a jihar zai lashe naira biliyan 8.631. Gwamna Bello Matawalle ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a yayin kaddamar da daya daga cikin uku na shirin RUGA a garin gwamnan dake hedikwatar karamar hukumar Maradun.
Ya tabbatar da cewa; za a gudanar da aikin a dukkanin yankuna uku na jihar, inda zai lashe naira biliyan 2.877. Sannan ya kara da cewa; kowanne yanki za a gina gidaje mai dauke da dakuna da kuma makarantun Islamiyya, da gonaki da masallatai da dam na ruwa.
Sannan za a gina ofishin ‘yan sanda da kuma shaguna 130 da karamar kasuwa, da kasuwar kiwo, cibiyoyin shakatawa da tituna da magudanan ruwa da sauran su. Matawalle, ya ce kafin kwanaki 100 na wa’adin mulkinsa zai tabbata ya assasa ginin RUGA din.