Gwamna Jahar Kaduna Nasir El-Rufa’i yayi jawabi akan matsayar Gwamnonin Arewa akan tsarin karɓa-karɓa na shugaban ƙasa.
A wani taro daya wakana a Kaduna, Gwamnonin sun ce tsarin karɓa-karɓa na shugaban ƙasa ya saɓawa kundin tsarin mulkin Nigeria
Sun bayyana haka, a matsayin maida martani ga buƙatar Gwamnonin Kudu na cewa dole Shugaban Ƙasa na gaba ya fito daga yankin su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda sun kama wani da ake zargin Mai Garkuwa da Mutane ne a Kano
A jawabin da ya yiwa ƴan jarida, El-Rufa’i yace
babu wani dazai zauna a Lagos ko Fatakwal, ya nuna yadda Arewa zata yi ko kuma wanda Arewa zata zaɓa.
Yace idan kudu suna son Shuwagabanci, to zama zata yi ta tattauna tayi da sasanci, sai ta a amince akan wanda za’a zaɓa, amma ba yin amfani da ƙarfi ko barazana domin karɓar mulki ba.
“Bama cewa babu tsarin karɓa-karɓa na shugaban ƙasa, ana iya yin haka, amma dole a zauna, dazai zauna ayi sasanci a Arewa, sannan sai mu bada goyon baya ga kudu, amma babu wani dake da ikon dazai zauna a Lagos ko a Fatakwal yace wai ko arewa tana so ko bata so, dole su bada kujerar shugabancin ƙasa ga kudu, wannan ba dai-dai bane, ba yanda muke siyasa bane, wannan ai shirme ne.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyyar ta ruwaito cewar El-Rufa’i shine Gwamna na farko, daya bada shawarar a bada miƙa ragamar shugabancin ƙasar ga kudu.
A shekarar 2020, yace cikin haɗin kai da adalci, ya kamata Arewa ta miƙa ragamar shugabancin ƙasar ga kudu, bayan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kammala mulki.
Wa’adin Mulkin Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari zai ƙare a shekarar 2023.