Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Dakta Asabe Vilita Bashir a matsayin Darakta Janar na Cibiyar Bunaksa Harkokin Mata ta Kasa wato NCWD a takaice.
Sabuwar Darakta Janar ɗin wacce ta fito ne daga Jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar nan, mashahuriyar yar siyasa ce, ta taba rike muƙamin Kwamishina a Jihar Borno har sau biyu, kana kuma Yar Majilisar Wakilai ce kazalika.
Dakta Asabe ta maye gurbin Barista Mary Ekpere-Eta ne wacce Wa’adin ta ke karewa a yau Asabar bayan shafe shekaru huɗu tana gwagwarmaya a cibiyar.
A Yanzu haka za ta shafe shekara huɗu ne akan kujerar, wanda jin dadin mulkin ta ka iya kai ta ga karin wani wa’adi.