By Abbas Yakubu Yaura
Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da ya sa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya dawo daga kasar Kenya zuwa Najeriya ranar Juma’a.
‘Yan Najeriya sun yi tsammanin zai je Birtaniya kai tsaye domin duba lafiyarsa bayan shirin kula da muhalli na Majalisar Dinkin Duniya daya cika shekaru 50 a birnin Nairobi na kasar Kenya, kamar yadda mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya sanar.
Adesina, yayin da yake sanar da tafiyar Buhari a kasar Kenya, ya ce shugaban zai zarce daga Nairobi bayan taron UNEP zuwa Burtaniya inda zai shafe tsawon makonni biyu don duba lafiyarsa.
Sanarwar ta ce “Daga Kenya, Shugaba Buhari zai tafi Landan domin duba lafiyarsa na yau da kullum wanda zai dauki tsawon makonni biyu.”
Sai dai a maimakon haka, shugaban ya koma Najeriya ne a ranar Juma’a da ya ba mutane da yawa mamaki, lamarin da ya kara rura wutar rade-radin cewa ya yi watsi da balaguron sa na zuwa Birtaniya.
Sai dai babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Mallam Garba Shehu, ya ce shugaban zai ci gaba da tafiya kasar Birtaniya.
Ya ce tun da farko ana sa ran shugaban kasar zai kammala tafiyarsa a ranar Asabar kafin ya wuce zuwa Najeriya, inda a ranar Lahadi zai fara tafiya zuwa kasar ta Birtaniya.
“Tsarin farko shine shugaban kasa zai kawo karshen ziyrar sa ta shirinsa a Kenya ranar Asabar,” Shehu ya shaida wa NAN.
“Babu wani abu da ya canza game da shirin tafiyarsa zuwa Landan; har yanzu yana nan kamar yadda aka tsara tun farko. Zai tafi Landon ranar Lahadi. Babu buƙatar kowane damuwa.
“Abin da ya faru shi ne shugaban ya iya kammala shirinsa a Nairobi tun da wuri fiye da yadda ake tsammani.
Shi ya sa ya dawo ranar Juma’a. Har yanzu zai tafi Burtaniya ranar Lahadi.”Yayin da yake kasar Kenya, Buhari ya halarci wani zama na musamman na bikin cika shekaru 50 da kafa Majalisar Dinkin Duniya.
Buhari ya ce, “Yayin da muke bikin cika shekaru 50 da kafuwar UNEP, muna yaba wa kokarin UNEP tare da karfafa daukar matakai don shawo kan sauyin yanayi, rabe-raben halittu, karuwar gurbacewar yanayi da sharar gida a matsayin manyan rikice-rikice uku da ke barazana ga duniyarmu.”
Shugaban ya kuma gana da Mista Ibrahim Thiaw, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na yaki da hamada a Nairobi.