Wani dan takarar gwamna a zaben 2019 a jihar Filato, Nura Tanko Waziri a jam’iyyar LP ya shawarci shugaban kasa da ya gaggauta bin umurnin kotun babban birnin tarayya Abuja, ya saki jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Zakzaky tare da biyansa diyya da kuma gina masa gida kamar yadda kotun ta bada umurni.
Dan takarar gwamnan ya bayyana hakan ne a wani Bidiyo da ya yadu a shafukan Sada zumunta, kuma Mujallar ta ‘yan shi’a da ake kira GWAGWARMAYA ta gani ta wallafa.
Mujallar ta ce, Nura Waziri ya ce; “Na yi niyyar ba shugaba Buhari shawara a matsayina na dan siyasa wanda ya kai matakin takarar gwamna a zaben da ya gabata. Watanni kadan ya rage mulki ya koma Kudu. Ya tabbata da cewa mutum daya ba ya shugabancin kasa, shawara ta a wurinka Buhari, ka jawo Dattijan Arewa wadanda suka kware a siyasa kamar irin su Tanko Yakasai, Ango Abdullahi, Hajiya Naja’atu, da sauran su, domin su ba ka shawarwari yadda zaka yi amfani da sauran watannin nan da suka rage domin kawo wa Arewa ci gaba.” Inji shi.
Dan siyasar ya ci gaba da cewa; akwai bukatar daga darajar masarautu domin su ci gaba da tattara al’umma waje daya domin al’umma ta samu natsuwa, sai dai dan siyasar ya ce; “Amma fa mabudin wannan aikin, shi ne sulhu da Malam Zakzaky. An yi abubuwa marasa dadi a Zariya, wanda ya jawo asarar rayukan ‘yan Nijeriya da yawa, Musulmai ‘yan arewa. An kashe Mazaje 548, mata 297, yara kanana 193, mata masu ciki 23, iyalai wanda ya hada da Uwa da Uba da ‘ya’ya guda 39. An kuma binne mutane guda 347. Ya za a yi Allah ya yi farin ciki da wannan abin?”
Nura Waziri ya kara da cewa; “Wannan yana daya daga cikin abubuwan da suka jawo ma ‘yan Arewa shiga cikin wannan matsala da ake ciki. Kididdiga na duniya ya nuna cewa; Arewa mun fi kowa Talauci, sannan ran dan Arewa shi ya fi arha a duniya gaba ki daya. Rashin sulhu da Malam Zakzaky zai sanya ka gama mulkinka a cikin damuwa. Kuma ka tashi a lahira da jinanan Muminai a hannunka. Ka yi tunanin wannan!”
Dan takarar gwannan, Nura Waziri bai tsaya nan ba, ya kara da cewa; “Ya kamata ka fara da bin umurnin kotu da suka bayar akan Malam Zakzaky. Ka sake Shi, ka biya Shi diyya, ka ba Shi gida a inda ya bukata. Sannan ka ba shi tsaro har zuwa lokacin da ya bukata. Ta haka ne watakila Allah zai ji tausayin kasarnan musamman mu mutanen Arewa ya sassauta mana saboda mu fita daga cikin damuwowin da muke ciki.” Ya tabbatar.
Dan siyasar ya ce ya bai wa shugaban kasa Manjo Janar Buhari wannan shawarar ne saboda sanayya da kuma tausayin Talakawan Arewa.
“In kunne ya ji, jiki ya tsira.” Ya karkare.