Asiwaju Bola Tinubu jigo a jam’iyyar APC ya ce akwai bukatar shugaba Muhammadu Buhari ya zage damtse sosai wajen bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.
Tinubu ya ce har yanzu tattalin arzikin kasar yana da rauni duk da cewa kasar ta fice daga durkushewar tattalin arziki.
Tinubu ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a taron tunawa da Sardaunan Sakkwato, Marigayi Sir Ahmadu Bello da aka yi a Kaduna ranar Asabar.
Hukumar kididdiga ta kasar a watan Fabarairun da ya gabata ta sanar cewa arzikin da kasar ta ke samar wa cikin gida ya karu da kashi 0.11 a karshen wata hudu na shekarar 2020.
A cewar hukumar ta NBS, ci gaban ya nuna cewa tattalin arzikin kasar ya farfado daga koma bayan da ya samu. Sai dai a jawabin da ya yi lokacin da ya gabatar da wata takarda mai taken “Rage yawan kudin da ake kashewa kan shugabanci don ci gaban kasa da matasa a arewacin Najeriya bayan annobar korona”, Tinubu ya ce har yanzu da sauran rina a kaba.
Tsohon gwamnan jihar Legas ya ce duk da matakan da gwamnatin shugaba n kasa Muhammadu Buhari ta dauka, kawo yanzu tattalin arziki kasar yana da rauni saboda akwai mutane da dama da ba su da ayyukan yi.