A yau Talata Shuagban kasa muhammadu Buhari ya shiga wata ganawar sirri da gwamnonin jam’iyar APC mai mulki a fadar gwamnati dake babban birnin tarayya Abuja
Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyar ta APC na kasa kuma gwamnan jihar Kebbi ne ke jagorantar taron wanda ke gudana a dai lokacin da jam’iyar ke tsaka da neman shawarwari dangane da wanda zata fitar a matsayin mataimakin dan takaranta Asiwaju Bola Anmed Tinubu a zaben dake tafe.
Taron dai ya sami halartar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari, Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, Gwamnan Nasir Ahmed El-rufa’i na jihar Kaduna da dai sauran su.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Wasu jiga-jigan tsohuwar jam’iyyar CPC na son jam’iyyar APC ta zabi Ministan Shari’a, Abubakar Malami a matsayin wanda zai yi wa dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu mataimak a zaben shekarar 2023 dake tafe.