Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga wata ganawar sirri, tare da Shuwagabannin yankin Kudu maso Gabashin kasar na a Owerri Babban Birnin jihar Imo.
Taron Wanda akaki lamunce wa manema labarai su halar ta, ya na gudana ne a wani sabon zauren majalissar zartarwar jihar Imo, a fadar gwamnatin jihar dake Birnin Owerri.
Daga cikin wadanda suka halarci Taron akwai: Gwamnan jihar Ebonyi, David Umachi, Mataimakin Gwamnan jihar Abia Ude Okechukwu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bazan Dena yin Fim ba, Har’abada, inji Hadiza Kabara
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Shugaban Kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Farfesa George Obiozor, Ministan kula Harkokin kasashen Waje, Geoffrey Onyema, Karamin Ministan cikin gida Cif Uche Ogar, da sauran Su.
Tuni, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da titin Ihiagwa zuwa Nekede, ramin karkashin kasa na fasahar Balloon, tare da magudanar ruwa a hanyanyoyin Chukwuma Nwoha, Naze/ Nekede/ Ihiagwa Road, da na tagwayan hanyar Egbeada, da kuma sabbin gine-ginen zamani. Da gwamnan jihar Imo ya gina.
Comments 1