Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da ciwo karin bashin Dala biliyan 4 da kuma Yuro miliyan 710 daga waje.
Kudurin na kunshe ne a cikin wasikar da shugaban ya aike wa shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, wadda kuma aka karanta a zauren majalisar a yau Talata.
Buhari ya ce za a karbo rancen ne daga Bankin Duniya da Hukumar tallafawa ci gaban kasashe ta Faransa da kuma Bankin EXIM da ke Amurka da kuma Asusun Tallafawa Noma na Duniya IFAD.
Shugaban Nijeriyar ya ce rancen zai bai wa Gwamnatinsa damar aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa a sassa daban-daban.