Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar dokokin tarayya wata takarda dake bukatar ƙarin wa’adin shekarun ritaya ga malaman makaranta.
Shugaba Buhari na buƙatar a kara shekarun ne daga 60 zuwa 65, yayin da wa’adin masu yi kasa hidima kuma ke bukatar a kara daga 35 zuwa 40.
Har wa yau majalisar na ci gaba da nazari kan takardar nadi da shugaba Buhari ya aike mata dake neman ayyana Manjo Janar Faruk Yahaya a matsayin Hafsan Sojin Najeriya.
Faruk Yahaya idan majalisar ta tabbatar da shi zai maye gurbin marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ne da ya rasu sakamakon hatsarin Jirgin sama a Jihar Kaduna tare da wasu manyan jami’an soji.
A hannu guda kuma kakakin Majalisar wakilan tarayya Femi Gbajabiamila ya ce lamarin tsaron kasar nan na ci gaba da tabarbarewa ta inda ka iya komawa wani fagen yaƙi, don haka ne ya tilas majalisar ta yi nazari sauya salon taswirar tsaron kasar.