Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Birgediya Janar Yusha’u Ahmed a matsayin babban daraktan hukumar masu yi wa kasa hidima (NYSC).
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na NYSC, Eddy Megwa, ya tabbatar wa manema labarai a ranar Lahadi cewa Janar Ahmed zai fara aiki a hukumance a matsayin sabon DG ranar Litinin din nan.
KARANTA HAKANAN Hukumar NYSC Da CBN Zasu Hada Kai Don Yada Shirin E-naira
Megwa ya lura cewa Yusha’u Ahmed ne zai karbi ragamar mulki daga hannun Christy Uba wanda aka nada a matsayin mai kula da shirin bayan tsige shugaba na 18, Muhammad Fadah a watan Nuwamba 2022.
“Za mu fitar da sanarwa gobe. Za a gudanar da mika aikin ne ranar Litinin da karfe 11:30 na safe a shedikwatar NYSC da ke Abuja,” in ji shi.
Idan za a iya tunawa, a ranar 2 ga watan Satumba, 2022, wata wasika da shugabar hukumar ta NYSC, Fatima Abubakar ta rubuta, kuma ta rubuta wa ministar wasanni da ci gaban matasa, Sunday Dare, ta lissafo batutuwa da dama a kan shugaban hukumar, Muhammad Fadah.
Wasikar ta yi nuni da cewa wasu daga cikin korafe-korafen da ake yi wa Mista Fadah sun yi nuni da cancantar karatunsa da shekarunsa, inda ta kara da cewa tun da farko hukumar ta kira ta kuma yi magana da shugaban hukumar game da zargin “amma ya kasa cika alkawarinsa na sauya.”
Bayan jerin korafe-korafen, an cire Mista Fadah a matsayin DG wanda zai fara aiki daga ranar 16 ga watan Nuwamba 2022.
A Wani Labarin Kuma Al’ummar Igbo Mazauna Kano Sun Amince Da Atiku Abubakar
Shugabannin al’ummar Igbo da shugabannin kungiyar a Kano sun amince da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.
An bayyana hakan ne a yayin ziyarar tuntubar da mai fafutukar yakin neman zaben Atiku Abubakar a Kano, Alhaji Ibrahim Ali Amin Little ya kai wa Eze Ndigbo Na Kano Ikechukwu Oliver Akpudo a fadarsa.