Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada sabbin Sakatarori na dun-dun-dun guda 9 a Ma’aikatun gwamnatin tarayya daban daban.
Shugaban Ma’aikatan gwamnatin tarayya Dakta Folasade Yemi-Esan ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanar wa da ya fitar a yau Talata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutum 7 sun aje mukaman su a PDP
A cewar sanarwar da jami’in Hulda da jama’a na Shugaban Ma’aikatar Abdul-Ganiyu Aminu ya fitar, ta nuna cewar, wadanda aka nada sun hadar da: Mr Bitrus Bako Nabasu daga Ma’aikatar kula da albarkatun Man Fetur, inda aka Mai da shi Ma’aikatar sadarwa ta kasa, Dakta Evelyn Ngige daga ofishin Kula da Walwala zuwa Ma’aikatar Masana’antu kasuwanci da zuba hari.
Sauran sun hadar da: Mammam Mahmuda daga Ofishin Gudanarwa zuwa Ma’aikatar kula da kiwon lafiya, da Dakta Nasir Sani Gwarzo daga Ma’aikatar Masana’antu da zuba jari zuwa Ma’aikatar kula da albarkatun Man Fetur, Dakta Anthonia Akpabio Ekpa daga Ma’aikatar kula da harkokin Mata zuwa ofishin Kula da harkokin Gwamnati.
Sauran sabbin nade-naden sakatarori sun hadar da: Dakta Onwudiwe Maryanne Ngozi, da Dakta Ogunbiyi Marcus Olaniyi, da Yusuf Ibrahim Idris, da kuma Injiniya Adebiyi Olusesan Olufunso da aka sa su a Ofishin Kula da walwala, Ofishin gudanar wa, Ofishin kula da aiyuka, da kuma Ma’aikatar kula da harkokin Mata ta kasa ,duk kannin su.
A cewar sanarwar nadin na su, zai fara aiki ne nan take, sannan bika ragamar gudanar wa, da kuma amsar gudanar wan aiki, zai gudana ne a ranar 6 ga watan Ogustan shekarar 2021. Face na ofishin Babban sakataren Ma’aikatar kula da kiwon lafiya, da zai gudana a ranar 13 ga watan watan nan da mu ke ciki.