By Ishaq Dabai
A Lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika kasafin ku’din Shekara ta 2022 mai zuwa ga majalisu biyu na tarayyar Nageriya, wato majalisar dattijan Nageriya da majalisar wakilan Nageriya a Lokacin da yake bayyana jin da’dinsa Sanata Malam Uba Sani ‘dan majalisar dattijai daga kaduna ta tsakiya ya nuna farin cikin sa game da kasafin na wannan Shekara, inda ‘dan majalisar yace na shiga cikin Jerin takwarorina na Majalisar Dokoki ta kasa a yau domin karban bakuncin Shugaban kasarmu, Shugaba Muhammadu Buhari yayin da yake aiwatar da muhimmin aikin gabatar da Kasafin Kudi na shekarar 2022 kasafin mai taken tsarin ‘Dorewar Ci Gaban Tattalin Arziki.
Sanatan ya Kara da Cewa Lallai abin farin ciki ne cewa Shugaba yaci gaba da maida Hankali tare da yanke shawarar maido da gabatar da tsarin kasafin kudin watan Janairu zuwa ga Disamba. Kamar yadda ya gabatar da kasafin kudin a yau, Shugaba Buhari ya aike da sako ga ‘yan Najeriya cewa yana da sha’awar barin gadon mulkin da ingantaccen tsari daya aiwatar na kasafin kudi.
Kazalika yace yana so ya ƙarfafa abubuwan daya gada na ci gaban ababen more rayuwa.Kasafin Kudin 2022 ya kasance cike da kyakkyawan niyya da himma duk domin cimma wannan manufar.
Majalisar Dokoki ta Kasa, karkashin Jagorancin Sanatan (Dakta) Ahmad Lawan zai tabbatar tare da fara aiwatar da shirye-shiryen kasafin kudin, domin rattaba hannu tare da amincewa Muna sa rai kasafin zai sake daidaita tattalin arzikin Najeriya tare da fitar da ‘yan Najeriya masu tarin yawa daga kangin talauci. Inji Sanatan.
A satin daya gabata ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya aikewa da majalisar wasikar neman lamumcewa domin sake aro bashin Dalar Amurka Bilyan shida $6 domin cike gibin kasafin ku’din na shekarar 2022.