Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Nijeriya na fuskantar matsalar sauyin yanayi. Inda ya ce; “Nijeriya na da makwabtaka da kasashen da suke da sahara, a yayin da Lake Chad ke bushewa kuma yawan jama’a na karuwa.” In ji shi.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin da ya gana da wata kungiyar matasan Nijeriya akan sauyin yanayi kafin a ranar Juma’a a birnin New York na kasar Amurka kafin ya bar ta zuwa Abuja bayan ya halarci taron majalisar dinkin duniya na 74.
Shugaba Buhari ya ce ana fuskantar kalubale ta wannan fannin. Inda ake da karancin muhalli da kuma karancin ruwan sama, ya ce wadannan suna daga cikin matsalolin da kasar ke fuskanta.
Shugaban kasa ya jinjinawa matasan da suka wakilci Nijeriya a taron UNGA din kan sauyin yanayi, ya ce; yana da kyau su rika halartar irin wannan taron domin su fuskanci irin matsalolin da tsoffi ke fuskanta.