By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Abuja bayan halartar taron hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Afirka karo na 3 a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.
Shugaban wanda ya samu tarba ne a ranar Lahadi ta hannun shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Farfesa Ibrahim Gambari da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da sakataren dindindin na fadar gwamnati Alhaji Tijjani Umar a lokacin da suka isa fadar gwamnatin tarayya Abuja.
Sannan ya karbi katin zagayowar ranar haihuwa daga hannun shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, jami’in gudanarwa Alhaji Abubakar Maikano da sauran mataimaka jim kadan bayan dawowar sa.
Haka kuma ya dauki hotuna tare da dansa wanda aka yi wa sabon nadin rawani a matsayin Talban Daura, Yusuf Muhammadu Buhari da sauran mataimaka jim kadan bayan dawowarsa daga ziyarar aiki a birnin Istanbul.
Indan za’a iya tunawa Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a ranar Alhamis ne dai shugaba Buhari ya tashi daga Abuja zuwa Istanbul domin halartar taron hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Afirka karo na uku, wanda shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jagoranta.
Kazalika shugaban ya samu rakiyar uwargidansa Aisha Buhari da ministocin harkokin waje, Geoffrey Onyeama, da ministan Tsaro, Mejo Jar Bashir Magashi (mai ritaya) da ministan birnin tarayya FCT, Mohammed Bello, sai ministan Lafiya Dakta Osagie Ehanire, ministan Noma Mohammed Abubakar, sai na Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari Adeniyi Adebayo, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mejo Jar Babagana Monguno (mai ritaya) da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar.
Bayanan hakan na kushe a cikin wata sanarwa da mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar.