A yau Laraba ne shugaba kasa Buhari ya kaddamar da tambarin bikin cikar Nijeriya shekara 60 da samun ‘yancin kai.
Tambarin wanda yake kalar tutar kasar ne na dauke da sakon haɗin-kan kasa.
Shugaba Buhari ya kaddamar da wannan tambari ne a taron majalisar ministoci da ya jagoranta a yau Laraba a Abuja.