Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan a fadar shugaban kasa ta Aso Rock a yau Juma’a kan rikicin siyasar dake addabar kasar Mali.
Tsohon Shugaba Jonathan dai shine mai shiga tsakani na Kungiyar ECOWAS a kasashen nahiyar Afirka.
A jawabinsa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci dukkannin masu ru a da tsaki kan harkokin siyasa a kasar ta Mali da kowaya maida wukar sa kube don shawo kan rikice-rikicen dake addabar kasar.
Dama dai a shekaran Jiya ne Jagororin Mulkin Sojin Kasar ta Mali ta Kori Jonathan bayan da ya tashi takanas ta Kano zuwa kasar fon shiga tsakani.
To amma ya shaida wa shugaba Buhari cewa komai zai yi daidai a kasar ganin cewa Ƙungiyar ECOWAS na gabda gudanar da wani gagarumin taro kan wannan dambarwa.
Ya ce taron shugabannin kungiyar ya zamo wajibi a dai-dai wannan lokaci don ganin an kawar da wannan sa toka sa katsi tsakanin yan siyasar kasar da ma matsalolin dae addabar Afirka ta yamma baki daya.