By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Juma’a ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da tawagar shugabanni da sarakunan yankin Kudu maso Gabashin kasar nan.
Ya tarbi tawagar data kunshi shugabannin gargajiya da na addini na kabilar Igbo a fadar gwamnati dake Abuja.
Daga cikin shugabannin akwai tsohon gwamnan jihar Anambra, Chukwuemeka Ezeife; tsohon ministan sufurin jiragen sama, Mbazulike Amaechi da kuma tsohon shugaban kungiyar masu tunani ta Igbo, Ikenga Goddy Uwazurike.
Jami’an gwamnati a taron sun hada da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, da Ministan kimiyya da fasaha, da kirkire-kirkire, Ogbonnaya Onu l, da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Sauran sun hada da ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige; Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama da Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba.
Sai dai kuma ba a bayyana cikakken bayanin ganawar ba, yayin da tawagar ta ki yin magana da manema labarai na fadar gwamnati bayan Kammala taron.
Duk da haka, ba za a ce shugabannin sun tattauna batun tsaro a yankin Kudu maso Gabas ba.
Wani batu da ake ganin zai iya sa a gaba shine kamawa, tsare da kuma gurfanar da shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu.