Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa birnin Riyadh na kasar Saudiyya a ranar Litinin da misalin karfe 11:50 na dare, don halartar taron zuba jari.
Mataimakin gwamnan Riyadh, Yarima Mohammed bin Abdulrahman Abdulaziz ne ya tarbi shugaban a filin jirgin sama na Sarki Khalid.
Shugaba Buhari tare da wasu shugabannin kasashen duniya za su halarci bikin bude taron a yau Talata, Wanda da cikakken zaman taron na kwanaki uku da zai mayar da hankali kan taken taron karo na 5 “Zuba jari ga bil’adama”.
Ana sa ran shugaban kasar zai halarci taron saka hannun jari karo na 5 tare da shugabannin ‘yan kasuwa daga Najeriya, ma’aikatan banki, shugabannin masana’antu da masana makamashi don tattaunawa kan batutuwan da suka shafi makomar zuba jari a fadin duniya.
KARANTA WANNAN LA ARIN: Tubabbaun Yan bindiga sun Toshe Ofishin Gwamna Ayade
A cewar sanarwar tun farko kan taron, wanda kakakin shugaban kasar, Garba Shehu, ya fitar ranar Litinin a Abuja, taron na kwanaki uku, mai taken zuba jari a harkokin bil’adama, zai karbi bakuncin shuwagabannin duniya da masu kula da Manyan kadarori.