Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa Gwamna Rotimi Akeredolu na Ondo da iyalansa bisa rasuwar mahaifiyarsu mai kaunarsu, Misis Grace Akeredolu.
Shugaban ya bayyana ra’ayinsa ne a cikin sakon ta’aziyyar da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Mista Femi Adesina ya fitar ranar Juma’a a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Mahaifiyar Gwamnan Jam’iyyar APC Ta Rasu
Ya kuma bukaci ’yan uwan Akeredolu da su jajirce daga darussan rayuwa da mama ta koya musu, da dabi’un kulawa da tausayi da ta sanya a cikin su da sadaukarwar da ta yi domin ‘ya’yanta su samu nasara a rayuwa.
Buhari ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma bukaci ‘yan uwa da su yi riko da imaninsu da kuma dogara ga Allah ya yi musu jagora a cikin wannan mawuyacin hali. (NAN)
A wani labarin kuma, PDP Ta Nada Tambuwal A Matsayin Darakta Janar Na Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa
Jam’iyyar adawa ta PDP ta nada gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Tambuwal a matsayin shugaban sabbin jerin sunayen ‘ya’yan jam’iyyar na yakin neman zaben shugaban kasa (PCO).
Sauran wadanda aka nada a kungiyar sun hada da gwamnan jihar Bauchi, Mista Bala Mohammed da gwamnan jihar Oyo, Mista Seyi Makinde a matsayin mataimakan shugabannin shiyyar arewa da kudu.