By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Lahadi, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, da kuma ‘yan kasar Afirka ta Kudu bisa rasuwar Desmond Tutu, wanda ya lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya.
Wannan na zuwa ne a wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar mai taken ‘Buhari ya jajanta kan rasuwar Archbishop Desmond Tutu’.
A cewar Adesina, “A madadin gwamnati da al’ummar Najeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga shugaban kasar Cyril Ramaphosa, ‘yan kasar Afirka ta Kudu da kuma kungiyar Kiristoci ta duniya, musamman ma Anglican Communion, bisa rasuwar Archbishop Emeritus, Desmond Tutu, dan shekara 90, a ranar Lahadi, 26 ga watan Disamba 2021.
“Shugaba Buhari ya yi imanin mutuwar fitaccen malamin nan, mai fafutukar kare hakkin dan Adam, shugaban tunani, masani kuma mai taimakon jama’a, yana kara haifar da tazara a cikin duniyar da ke matukar bukatar hikima, mutunci, jajircewa da tunani mai kyau, wadanda halaye ne da kyautar Nobel ta zaman lafiya. Wanda ya ci lambar yabo, a shekarar 1984, an kwatanta da kuma misalta cikin kalmomi da ayyukan sa.”
“A matsayinsa na dan Afirka ta Kudu, dan duniya kuma fitaccen shugaban duniya, Buhari ya tabbatar da cewa irin rawar da Tutu ya taka wajen yaki da wariyar launin fata, da jure wa cin zarafi, dauri da kuma zaman gudun hijira na tsawon lokaci, ya dauke shi daga kan mimbari zuwa ga duniya, siyasa, da kuma dacewarsa.
Sannan yace ya samu Matsayi, a karkashin Shugaba Nelson Mandela, a jagorancin kwamitin gaskiya da sulhu ya ba da waraka da jagoranci ga kasarsa da duniya.
“Shugaban ya aike da ta’aziyyarsa ga Leah Tutu, matar shugaban ruhaniya kuma abokin tarayya a cikin gwagwarmayar rashin adalci, cin hanci da rashawa da rashin daidaito, dangin Tutu, hukumar da ma’aikatan gidauniyar Desmond da Leah Tutu Legacy Foundation, Dattawa da Ƙungiyar Laureate na Nobel, sannan yana mai kira ga muryar masani kuma malami, da ayyukansa da aka buga, da zantuka masu zaburarwa za su yi ta yawo cikin tsararraki, tare da kawo ƙarin haske da ga bambancin addini, dimokuradiyya da kyakkyawan shugabanci.
“Saboda haka, ya yi addu’ar Allah ya hutar da ran Archbishop Tutu, wanda rayuwarsa da zamaninsa suka aiko da sakon da ba za a mantawa da shi ba kan soyayya da gafara.”