By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da gidaje 76 a karkashin shirin samar da gidaje na kasa kashi na farko a Dutse babban birnin jihar Jigawa.
Aikin yana karkashin shirin samar da gidaje na kasa (NHP) na ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya da aka fara aiwatarwa a fadin tarayya.
Hukumar NCC Da Kamfanin Google Sun Hada Kai Don Kawo Sauyin Zamani A Najeriya
Gidajen sun ƙunshi sashi 4 na bungalow mai daki 1; sashe 24 na bungalow mai dakuna 3 da rukunin gidaje 48 na bungalow mai dakuna 2, wadanda aka bayar a watan Nuwambar shekarar 2016 a kan kudi Naira miliyan 727.4.
An bayar da kwangilar samar da ababen more rayuwa na aikin ne a watan Mayun shekarar 2017 kan jimillar kudi Naira miliyan 463.6. Tituna, magudanar ruwa da kammala kwalta sun lakume tsabar kudi kimanin Naira miliyan 294.3.
Kazalika Wutar lantarki tare da girka na’urar rarraba hasken wutar lantarki taransfoma mai karfin 500KVA sun lakume Naira miliyan 82.9 sannan rijiyar burtsatse da babur ta lakume Naira miliyan 86.3.
Buhari wanda Ministan Albarkatun Ruwa Suleiman Adamu ya wakilta, ya bayyana gina rukunin gidaje a jihohi 35 na tarayya a matsayin misali mai kyau na wasu hanyoyin ci gaba da hadin gwiwar gwamnatocin za su iya samarwa.
Ya ci gaba da cewa kaddamar da aikin ya mayar da martani ne ga ‘yan Najeriya da ke da burin mallakar gida, yana mai cewa yana da kwarin gwiwar cewa idan aka samar da filaye da yawa gwamnatin tarayya za ta iya yin hakan.
Sakataren dindindin na ma’aikatar, Dr Bashir Nura Alkali, ya bayyana cewa ma’aikatar ta samu nasarar gina gidaje a karkashin shirin a jihohi 35, banda Legas.
Alkali wanda ya samu wakilcin ko-odinetan shiyyar Arewa maso yamma Emmanuel Hangeior, yace falsafar da hukumar ta NHP ta kafa shine samar da tsarin gwajin mai araha, mai saukin kai da karbuwa kamar yadda dokar gidaje ta kasa ta kunsa.
Comments 2