Daga: Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon tambarin kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), wanda ke nuni da cewa kungiyar ta tashi a matsayin wata cibiyar kasuwanci mai riba wacce za ta bayyana rabe-rabe ga masu hannun jarin ta.
Shugaban ya gudanar da bikin ne a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Talata, a wani biki da ya samu halartan manyan jami’an gwamnati da wakilan kasashen duniya da masu ruwa da tsaki a harkar man fetur da iskar gas.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/atiku-ya-taya-peter-obi-murnar-cika-shekaru-61-a-duniya/
Sabon tambarin da ya kaddamar na da taken, “NNPC: Makamashi don yau, Makamashi don gobe.” (“NNPC: Energy for today, Energy for tomorrow.”)
Da yake jawabi a wajen taron, shugaba Buhari ya bayyana jin dadinsa da cewa a kodayaushe yana samun damar tsara yadda harkar man fetur ta kasancewa a kasar nan.
Ya godewa Majalisar Dokoki ta kasa bisa yadda ta taimaka wajen ganin an amince da dokar masana’antar Man Fetur (PIA), wadda ta dade tana aiki a kan gwamnatoci daban-daban amma sai a wannan lokacin ake aiki da ita a yanzu.
A Wani Labarin Kuma Dan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar APC mai mulkin kasar, Bola Tinubu, zai gabatar da tsohon gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima ga al’umar kasar nan a matsayin mataimakinsa a zaben shekarar 2023.
Wata sanarwa da jam’iyyar APC mai mulki ta kasa ta wallafa a shafinta na Tuwita ranar Talata da safe ta ce za a gabatar da Sanata Shettima ne, a gobe Laraba.
Sanarwar ta yi nuni da cewa, “A hukumance jam’iyyar APC za ta gabatar da dan takarar mataimakin shugaban kasarta, Sanata Kashim Shettima, ga al’ummar Najeriya ranar Laraba, 20 ga watan Yulin shekarar 2022.
Za a yi bikin gabatar da shi ne a babban dakin taro na Shehu Musa Yar’Adua da ke bababn birnin Tarayya Abuja da misalin karfe 11 na safe.
Idan ba’a nanta ba dai A makon jiya ne Bola Tinubu ya sanar da zaben tsohon Gwamnan Jihar Borno kuma Sanata mai wakiltar Mazabar Borno Ta Tsakiya, Kashim Shettima, a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a babban zaben shekarar 2023 mai zuwa..
Sai dai awanni ashirin da hudu da fitar da sanarwar daukar Shattiman, batun ya jawo muhawara mai zafi inda wasu ke ganin bai dace Tinubu, wanda Musulmi ne daga yankin kudancin Kasar nan, , ya zabi Shettima, wanda Musulmi ne daga Arewacin Najeriya a matsayin mataimakinsa ba.
Amma jam’iyyar APC da ma Tinubu sun ce zabensa ba shi da alaka da addini.
Shettima gogaggen ɗan siyasa ne wanda ya daɗe yana jan zarensa a siyasa musamman a arewa maso gabashin kasar nan.
An haife tsohon ma’aikacin bankin a ranar 2 ga watan Satumbar 1966 kuma ya yi karatu a Jami’ar Maiduguri da kuma Jami’ar Ibadan.