A wani mataki na nuna juyayi da alhini, gami da nuna damuwa da damuwar al’ummar ta, gwamnatin tarayya ta tura wata tawaga izuwa Jihar Adamawa don gudanar da ta’aziyar tadangane da rasuwar tsohon Minista a tsohon arewacin Najeriya Alhaji Abdullahi Danburam.
Cikin jiga-jigan mutane dake cikin tawagar akwai Ministan birnin tarayya Abuja Muhammad Bello da ministan harkokin noma Alhaji Sani Shanono gami da babban mai tallafawa Shugaba Buhari kan yada labarai Mallam Garba Shehu.
Sauran sun haɗa da babban mai tallafa wa shugaba Buhari kan harkokin cikin gida Muhammad Sarki Abba, da dai sauran manya kuma jigogin jami’an gwamnati.
Da yake jawabi a madadin tawagar, Ministan Birnin tarayya Abuja Muhammad Bello shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya umarce su da su tashi tanakas ta Kano don isar da ta’aziyar su ga al’ummar ta Adamawa bisa rasuwar ta Danburam.
Da yake maida hawabi, gwamna Ahmadu Fintiri ya nuna jin dadinsa bisa wannan irin karamci da shugaba Buhari ya nuna wa al’ummar Adamawa inda yaa ce lallai bai mance da su ba.
Marigayi Abdullahi Danburam ya rigaye mu gidan gaskiya ne a babban asibitin tarayya daje birnin Yola na Jihar Adamawa bayan fama da wani gajeren rashin lafiya.
Shi dai Danburam mai kimanin shekara 87 ya rasu ne ya bar ƴaƴa sha bakwai da jikoki 55 da kuma tattaɓa kunne 49.