Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karbi sakon maganin warkarwa da kuma rigakafin cutar Korona da kasar Madagascar ta samar.
Buhari ya amshi sakon na maganin wanda aka yiwa suna da ‘Covid-Organics’ da Madagascar ta aika zuwa Nijeriya ta hannun shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embalo, wanda a ranar Asabar suka gana da shugaba Buhari a Abuja.
Cikin sakon da ya aike ta hannun Bashir Ahmad, mataimakinsa kan kafafen sadarwa na zamani, shugaba Buhari yac e kamar yadda ya yi alkawari a baya, kwararru daga fannin kimiyyar zamani da kuma gargajiya a karkashin jagorancin hukumar tantance ingancin abinci ta magunguna ta Nijeriya, NAFDAC, za su gudanar da karin bincike kan maganin na ‘Covid-Organics’ kafin soma amfani da shi kan masu cutar Korona a kasar.
Tuni dai wasu kasashen Afrika suka karbi maganin na ‘Covid-Organics’ ciki harda Nijar da kuma Tanzania.