Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yanzu ma’aikatar jin kai da lura da ibtila’o’i da ci gaban al’umma an kirkireta bisa nasarar da gwamnatin tarayya ta samu kan shirin tallafawa na musamman wanda aka fi sani da SIPs na naira biliyan 500.
Buhari ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa da ya yiwa ‘yan kasa a yau Talata domin tunawa da Nijeriya cika shekara 59 da samun ‘yancin kai a Abuja. Ya tabbatar da cewa shirin na SIPs zai ci gaba da tallafawa Talakawa.
Buhari ya kara da cewa tallafin na naira biliyan 500 zai ci gaba da bai wa daliban makarantun firamare abinci, da kuma tallafawa masu kananan sana’o’i da masu dogaro da kawukansu tare da daukar ma’aikata a karkashin N-Power da ba da basussuka da sauran su.
“Mun kirkiri ma’aikatar jin kai da kuma lura da ibtila’o’i da ci gaban al’umma domin lura da wannan fannin” In ji Buhari. Ya ce wadanda suka amfana da wannan shirin, yana mai tabbatar musu da cewa za su samu ci gaba bisa wannan tallafi.
Wannan jawabi na shugaban kasa ya sanya masana na ganin an sake ragewa mataimakin shugaban kasa wato Muhammadu Buhari karfin iko, domin kafin a kirkiri wannan ma’aikata, shirin na SIPs, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo shi ne yake jagorantar wannan shiri.
Hakan na nufin shugaban kasa ya rage ma mataimakinsa karfi ke nan tunda ya mika wannan aiki ga sabuwar ma’aikatar da shugaban kasar ya kirkira?
Wannan shi ne tambayar da kowa ke yi.