Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya koma birnin tarayya Abuja bayan shafe kwanaki takwas yana hutu a mahaifarsa Daura.
Gabannin tashin a ranar juma’a zuwa Abuja, shugaba Buhari ya samu karramawa daga rundunar sojin Najeriya karkashin runduna ta 17 da ta 213 ta Forward Operating Base.
Har wa yau gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da mataimakinsa Mannir Yakubu da Kakakin Majalisar dokokin jihar gami da manyan jami’an gwamnati duk su raka shugaba Buhari zuwa filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua don yin bankwana.
Da ma tun a frakon makonnan ne shugaba Buhari ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin tarayya da na jiha suka kammala a jihar ta Katsina.
Idan ba a manta ba dai shugaba ya bi sahun dumbin musulmin jihar wajen gudanar da bukukuwar Babban Sallah da ya gudana a makon da ya gabata.
Kazalika yan yiwa kasa hidima da aka tura jihar sun ziyarci shugaba Buhari don taya shi murnar Sallar inda ya musu goma na arziki ta hanyar basu shanu guda biyu da tsabar kudi har naira miliyan guda.