By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya mika sakon ta’aziyya ga dan majalisar da ke wakiltar mazabar Oyo ta tsakiya, Teslim Folarin, da ‘ya’yansa, da ‘yan uwa da abokan arziki wadanda suka yi alhinin rasuwar matar Sanatan, Angela Folarin.
Sakon ta’aziyyar Buhari na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu a yammacin Juma’ar da ta gabata ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina, mai taken ‘Shugaba Buhari ya yi wa Sanata Folarin ta’aziyyar rashin matarsa, Angela.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Addu’a da tunanin shugaban kasa suna tare da ‘yan Folarin yayin da suke nuna alhinin rabuwar matar aure da uwa, inda ya bukace su da su samu natsuwa da kwarin guiwa a kan gaskiya cewa Allah Madaukakin Sarki yana tare da mu a cikin yanayi mai kyau da wahala na rayuwa.”