Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Alhaji Sabiu Abubakar da kuma Oba Oluniyi a matsayin wadanda za su rike mukaman mataimakan kwamishina a Hukumar Inshora ta NAICOM.
Rasaaq Salami, shugaban hukumar NAICOM din ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Abuja a ranar Litinin.
A cikin sanarwar an bayyana cewa; Abubakar zai zama mataimakin kwamishina a bangaren ‘Technical’ yayin da Oluniyi zai zama mataimakn kwamishina mai kula da gudanarwa a ‘F&A’.
Nadin na su zai fara aiki ne daga ranar 17 ga watan Yuli za kuma su kasance a kan mukamin har zuwa shakara 5 masu zuwa