By Ishaq Dabai
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar alhamis ya nemi majalissar dainkin duniya ta sanya hannu a shirin sake tsugunar da ‘yan gudun hijira a arewa maso gabas na najeriya.
Ya yi wannan maganar ne a Fadar sa a Abuja, yayin da ya karbi bakuncin Ahunna Eziakonwa, Shugaban Ofishin Yankin Afirka na UNDP. Buhari yace UNDP ta cancanci yabo saboda taimakon data bawa Najeriya ta hanyoyi daban -daban, musamman wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas.
Sannan ya kara da cewa gwamnatinsa tana iyakacin kokarinta na gyara sansanonin ‘yan gudun hijira da mayar da su gidajen kakanninsu, amma ya lura cewa da dan albarkatu, taimako daga hukumomi kamar UNDP zai taimaka.
Kazalika ya gode wa Eziakonwa haifaffen Najeriya saboda ziyarar aikin data kai, “da kuma dawowar ta gida,” tare da lura da cewa ita kanta, Dakta Ngozi Okonjo-Iweala ta Kungiyar Ciniki ta Duniya, da Amina Mohammed, Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Najeriya tana alfahari dasu a duniya.