A kasa da mako guda da rasuwar shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa, Abba Kyari, shugaban kasa Buhari ya sake yin wani rashin a inda wani dogarinsa mai suna Lawal Mato shima ya rasu.
Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu, shi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu ya kuma fitar a ranar Talata a Abuja.
A cewar Garba Shehu, Mato ya rasu ne bayan ya kwashe shekara uku yana fama da cutar suga.
Dogarin na shugaban kasa Buhari ya kasance tare da Buhari tun kafin darewar shugaba Buhari kan mulki a shekarar 2015, inda shugaba Buhari ya bayyana shi a matsayin mutum mai kwazo da gaskiya. A karshe ya yi masa addu’ar Allah ya jikansa yasa aljanna makoma.