Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin babban kwamandan sojojin kasar nan ya sanya hannu kan wani gagarumin aikin soji a jihar Neja.
Jihar na fuskantar ci gaba da kai hare-hare a kan al’ummarta daga ‘yan bindiga da ragowar ‘yan ta’addan Boko Haram da ke tserewa sakamakon barazanar yaki a yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabashin kasar nan.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai.
A cewar Shehu, a cikin umarnin da ya aikewa shedkwatar tsaro a kwanakin baya, shugaban ya bukaci sojoji da su mayar da martani mai tsauri kan lamarin kashe-kashe da sace-sacen jama’a a jihar tare da samar da dabarun da aka sa a gaba ta hanyar amfani da karfi.
A sakonsa ga gwamnati da al’ummar jihar Neja, shugaba Buhari ya ce, “Ina so in mika sakon ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar sakamakon matsalolin tsaro da suka faru a baya-bayan nan.
A cewar sanarwar, shugaban ya sake nanata cewa tsaro wani nauyi ne da ya rataya a wuyan kowane dan kasa kuma ta hanyar hadin kai da hadin gwiwa da jami’an tsaro ne za mu iya shawo kan matsalolin a karshe.
“Gwamnatin tarayya a shirye take ta karfafa goyon baya da hadin gwiwa da dukkan jihohin. Na yi imanin cewa tare da cikakken hadin kan ’yan kasa, tabbas za mu shawo kan wannan matsala,” in ji Shugaban.