Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan ya shafe kwanaki 16 domin halartar manyan tarurrukan kasa da kasa guda uku a kasashen Scotland da Faransa da kuma Afirka ta Kudu.
Shugaban ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin karfe 4:45 na yamma, bayan ya halarci bikin baje kolin kasuwanci tsakanin kasashen Afirka karo na biyu na shekarar 2021, a birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu.
Ya bar Najeriya zuwa birinin Glasgow, na kasar Scotland, a ranar Lahadi, 31 ga Oktoban shekarar 2021, don halartar taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya (COP26) karo na 26.
Shugaba Buhari ya bar Glasgow domin halartar taron zaman lafiya a birnin Paris (PPF) na kasar Faransa.