Shugaban Kasa Muhammadu ya nada Alhaji Balarabe Shehu Ilelah a matsayin sabon shugaban hukumar kula da kafafen watsa labarai ta kasa wato NBC.
Ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Muhammad shi ya sanar da haka a wata Sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Juma’a.
Alhaji Shehu Ilelah zai rike ragamar hukumar ce na tsawon shekara biyar a wa’adin farko.
Wannan sauyi da aka samu na zuwa ne yan kwanaki bayan da tsohon shugaban riko na hukumar wato Armstrong Idachaba ya bada umarni wa kafafen watsa labarai da su rufe shafukan su na Tuwita.