By Abbas Yakubu yaura
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tashi daga Abuja ranar Laraba domin halartar taron Expo 2020 a Dubai dake Hadaddiyar Daular Larabawa.
Wannan dai na zuwa ne sa’o’i bayan daya karbi bakuncin shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa a fadar gwamnati dake Abuja, inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan ci gaban matasa tare da kaddamar da tattaunawar matasan Najeriya da Afirka ta Kudu.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan a wata sanarwa mai taken ‘Shugaba Buhari zai halarci taron Expo 2020 Dubai.
A cewar Adesina, EXPO 2020 Dubai mai taken, ‘Haɗin kai, Ƙirƙirar makoma,’ ya samar da yanayi ga Najeriya don shiga cikin ƙasashe sama da 190 don kulla haɗin gwiwa na gaskiya da ma’ana “don gina kyakkyawar makoma ga kowa.”
Ya kara da cewa, baya ga rangadin da za a gudanar a babban dakin baje kolin na Najeriya a bikin baje kolin da za a yi a ranar Juma’a, ranar kasa ta Najeriya, shugaban zai karbi bakuncin masu son zuba jari, da kuma ganawa da yarima mai jiran gado na Abu Dhabi da mataimakin koli na rundunar sojojin Hadaddiyar Daular Larabawa, Mohamed bin. Zayed Al Nahyan; da Mataimakin Shugaban kasa kuma Firaministan Hadaddiyar Daular Larabawa kuma mai mulkin masarautar Dubai, Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum.
“A ranar Asabar, Buhari zai kasance babban bako na musamman a dandalin kasuwanci da zuba jari na musamman. An hada shi ne don nuna kasancewar Najeriya a taron da Ma’aikatar Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari ta yi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Ana sa ran shugaban kasa muhammadu Buhari zai dawo Abuja a ranar Lahadi, 5 ga watan Disamba, 2021.”