Shugaban kasan Muhammdu Buhari ya taya dan takarar jam’iyyar APC a jihar Bayelsa, David Lyon murnar nasarar lashe zaben gwamnan da aka yi a jihar ranar Asabar din da ta gabata.
Buhari ya taya shi murnar ne a cikin wata takarda da mai magana da yawunshi, Femi Adesina ya fitar ranar Litinin a Abuja.
Shugaban kasan ya yaba wa magoya bayan jam’iyyar a jihar da suka fita don kada kuri’arsu duk da ‘yan tashe-tashen hankula da aka asamu a wasu sassan jihar a lokacin zaben.
A lokacin da yake Allah wadai da kashe-kashen da aka yi , shugaban ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon zaben.
Ya yaba wa jami’an hukumar INEC da jami’an tsaron da suka yi bakin kokarinusu wajen tabbatar da an yi adalci a zaben.
Ya bayyana tarzoman da aka yi a lokacin zaben a matsayin, “wani abu da ‘yan siyasa suka dauki nauyi”.
Shugaban kasan ya ce yana fatan za su yi aiki tare da sabon Gwamnan don inganta rayuwar al’ummar Bayelsa.
Shugaba Buhari ya kuma yi kira ga David Lyon da ya tabbata ya tafi da kowa a cikin mulkinshi sannan kuma wadanda bas u aminta da sakamakon zaben ba su je kotu.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana dan jam’iyyar APC David Lyon a matsayin wanda ya lashe zaben ne bayan ya yi nasarar samun kuri’u dubu dari 352,552.