Shugaban kasa Buhari ya taya Ngozi Okonjo Iweala murnar zama shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya (WTO).
A yau Litinin ne aka tabbatar da tsohuwar ministar kuɗin ta Nijeriya a matsayin mace kuma ‘yar Afirka ta farko da za ta jagoranci ƙungiyar bayan kusan wata shida ana ja-in-in-ja.
“A madadin Gwamnatin Tarayya da dukkanin ‘yan Nijeriya, Buhari na taya tsohuwar ministar kuɗi, Dr Ngozi Okonjo-Iweala, murnar zaɓenta a matsayin shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya,” a cewar sanarwar da Garba Shehu mai magana da yawunsa ya fitar.
Buhari ya ce ta jawo wa Nijeriya “kwarjini da girmamawa”, yana mai cewa ta aiwatar da sauye-sauye masu yawa lokacin da take ministar kuɗi da kuma ministar harkokin waje.