Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, ya yabi Shugaban Ƙasar Turkiyya, Shugaba Recep Tayyib Erdogan, daya buɗe iyakokin ƙasar sa, domin baiwa ƴan gudun hijira damar shiga ƙasar don karɓar tallafin jinƙai.
Buhari wanda yayi jawabi a wani taron haɗaka a Abuja, yace Erdogan ya zama misali ga duniya akan yadda ya kamata su riƙa kula da ƴan gudun hijira.
Mai ba Shugaban ƙasa Shawara akan Kafafen Yaɗa Labaru Femi Adesina ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun yi Garkuwa da Mutane 830, a jihar Kaduna cikin Wata 3
Adesina ya naƙalto Shugaban Muhammad Buhari na cewa, “ina yabawa da shugabancin ka da ka karɓi baƙin haure har miliyan 4, da suka gudo sakamakon faɗa a ƙasashen da ake yaƙi da Iraqi, da Syria, da Afghanistan. Ka zama abun misali ga sauran ƙasashen duniya.”
Yace Shugaba Buhari ya bayyana ziyarar kwanaki biyu da Shugaba Erdogan da matarsa Emine Erdogan, suke yi a matsayin wani cigaba da ƙawancen ƙasar Nigeria da Turkiyya.
Yace Buhari ya bayyana cewar wannan shine karo na biyu dana karɓi ɗan uwana a Abuja.
Akan ziyarar, Shugaba Buhari yace ” sun tattauna akan al’amura da dama da zasu inganta ƙawancen Nigeria da Turkiyya.
Erdogan zai kuma tattauna da haɗakar wani taro tsakanin Turkish da Nigeria, kafin ya bar Nigeria.
A jawabinshi, Shugaba Erdogan ya jaddada cewa ƙasar Turkiyya a shirye take ta inganta ƙawancen ta da Nigeria, har zuwa wani matsayi na ƙoli.
Erdogan ya kuma bayyana jindaɗin sa na yadda akwai ƴan Nigeria da dama dake karatu a ƙasar Turkiyya, da kuma amfana da tallafin karatu.
Comments 1