Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bacin ranshi, game da kisan gillar da a kayi wa wasu yan kasa, da suka hada da, wani jagoran Sakai, da Sarkin kyauyen Dabna dake karamar hukumar Hong na jihar Adamawa.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, ta hannun Babban mai bashi shawara a kan kafafen yada labarai Malam Garba Shehu, a jiya Alhamis a babban birnin tarayya Abuja.
Shehu ya ce, Shugaban kasa na Maida martani ne, dangane da lamarin da ya faru a jihar Adamawa a ranar Larabar ta gabata.
Buhari ya ce, “Wannan lamari na cin zarafin al’uma da kuma jefa rayuwar su cikin hadari, ba zaitafi haka kawai ba”inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutum 4 Yan gida daya sun mutu bayan sunci abinci Mai guba
Kana shugaba Buhari ya umarci dukkannin hukumomin tsaro da suyi gaggawar kai martani, ga dukkan masu kawo barazanar tsaro a fadin kasar nan.
“Bazamu lamunci kashe al’umar Naijeriya ba, da kare rayukar su ke hannun mu” a cewar shi.
Kazalika Buhari ya umarci Ma’aikatar jinkai da magance iftila’i ta kasa, da ta gaggauta kai dauki ga yankin da lamarin ya shafa.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, Babban mai bai taimakawa shugaban kasan, ya tabbatar da afkuwar lamarin, a cikin sanarwar da ya fitar.
Comments 1