Baba Buharin ya yi wannan kurarin ne jiya a wurin taron Kungiyar Kasashen Musulmi ta OIC, da ke gudana a kasar Saudi Arebiya a lokacin da yake tattaunawa da Shugaban Kasar Chadi Idrees Debi.
Buhari ya ce bayan sun koma gida, zai samu tattaunawa da Debin sosai da kuma sauran Shugabannin kasashen yankin domin murkushe Boko Haram da karfin tuwo.
Idan dai za a iya tunawa, Shugaba Buhari ya yi irin wannan barazanar a farkon mulkinsa. Sai dai maimakon ya murkushe Boko Haram din, sai ma ta cigaba, har ma aka sami karin masu garkuwa da jamaá.