Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wani ganarwar sirri da manyan jami’an tsaron kasarnan da yammacin yau Talata. Cikin wadanda shugaban kasar ya gana da su sun hada da; shugaban hukumar tsaro ta kasa ta NIA, Ahmed Rufai-Abubakar, Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Mohammed Adamu, da kuma mai ba shi shawara akan harkokin tsaro, wato NSA Mai Ritaya Babagana Mongonu.
Ya zuwa yanzu babu takamaimen ko me shugaban kasar ya tattauna da su. Amma dai rahotanni na ganin shugaban kasar zai gana da su ne saboda matsalar tsaron da ake fuskanta a kasarnan. Tare da kuma kisan ‘yan Nijeriya a Afrika ta Kudu.